Kun san sharuɗɗan tantance ministocin Nigeria ?

Sanata Saraki ya ce za su bi ka'ida wajen tantance ministoci
Bayanan hoto, Sanata Saraki ya ce za su bi ka'ida wajen tantance ministoci
An wallafa

Majalisar dokokin Nigeria ta gindaya sharuɗɗan da za ta bi wajen tantance mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya aika domin nada su a matsayin ministoci.

Daya daga cikin sharuɗɗan shi ne cewar duk wanda za a tantance sai ya nuna takardar bayanin dukiyar da ya mallaka.

Mai magana da yawun majalisar dattijan, Sanata Dino Melaye wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, ya kara da cewar dole ne sai sanatoci biyu daga jihar mutum na asali sun amince da shi, kafin majalisar ta amince a nada mutum a matsayin minista.

A ranar Talata, 13 ga watan Oktoba ne, majalisar ta ce za ta soma tantance mutanen.

Fashola na cikin wadanda buhari yake son ya bai wa minista
Bayanan hoto, Fashola na cikin wadanda buhari yake son ya bai wa minista

A makon da ya wuce ne shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dattijai sunayen mutane 21 domin a tantance su kafin, ya nada su a matsayin ministoci.