GSK ya yarda a kwaikwayi maganinsa a Afirka

GSK ya yarda a kwaikwayi magungunansa a AFrika
Bayanan hoto, GSK ya yarda a kwaikwayi magungunansa a AFrika
An wallafa

Kamfanin ya ce ba zai yi amfani da kalmar hakkin mallaka a kan magungunan ba domin kananan kamfanonin Afirka su samu damar yin magunguna masu saukin farashi.

Sai dai kuma GSK din ya ce zai bai wa wasu kamfanonin magani lasisi a kasashe masu matsakaicin arziki, a inda kuma za su rinka biyan kamfanin wasu 'yan kudade.

Sakamakon gasa tsakanin kamfanoni masu kwafar magunguna ne ya sanya farashin magungunan cutar HIV suka fadi.