Niger: Bam ya fashe a Diffa

Kungiyar Boko Haram sun sha kai hare-hare a Jihar ta Diffa.
Bayanan hoto, Kungiyar Boko Haram sun sha kai hare-hare a Jihar ta Diffa.
An wallafa

A jamhuriyar Nijar, rahotanni daga jihar Diffa na cewa wasu mutane 4 sun rasa rayukansu sakamakon tashin wani abu da ake zaton bam ne cikin wata motar daukar fasinja.

Lamarin ya afku ne yau da safe a wani kauye mai suna Ngarwa, wanda ke kimanin kilomita 22 daga gabashin Diffa a bisa hanyar Gigmi.

'Yan gudun hijira kimanin 150,000 daga Najeriya ne ke zaune a yankin domin tserewa hare-haren da Boko Haram ke kai musu.

'Yan kungiyar Boko Haram sun sha kai hare-hare a Jihar Diffa, inda suka kashe mutane da dama.