ZTE ya samu koma baya

An wallafa

Farashin hannun jarin kamfanin wayar salula da na'urorin sadarwa na China ZTE ya faɗi da kashi 11.7 bayan kamfanin ya koma kasuwar hada-hadar karon farko a wannan watan.

Tun daga ranar 7 ga watan Maris ne kamfanin ya nemi a dakatar da hada-hadar hannun jarinsa.

Kamfanin ya faɗa cikin rikici ne tunda ya fuskanci ƙalubale daga hukumomin Amurka dangane da hulɗa da Iran.

ZTE shi ne kamfanin samar da na'urori da suka shafi sadarwa ta waya na biyu mafi girma a China.

An fi sanin kamfanin ne da yin wayoyin salula na zamani, amma kuma ya na samar da na'urorin sadarwar wayar salula.