Shugaban Niger ya nada sabbin Ministoci

A watan da ya gabata ne Muhammadou Issoufou ya lashe zaben kasar
Bayanan hoto, A watan da ya gabata ne Muhammadou Issoufou ya lashe zaben kasar
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Shugaban kasar Nijar Muhammadou Issoufou ya nada sabuwar gwamnatinsa mai mambobi 38 karkashin jagorancin Firai minista Briji Rafini.

Wasu daga cikin manya manyan kalubalan da ke gaban majalisar ministocin nasa dai sun hada da hada kawunan 'yan kasar, da yin aiki tukuru domin habaka tattalin arziki da kyautata jin dadin rayuwar 'yan kasa.

Sai dai wasu kungiyoyin farar hula da ma talakawa na ganin adadin ministocin ya yi yawa idan aka yi la'akari da cewa Nijar kasa ce mai raunin tattalin arziki.

Ga rahoton da Baro Arzika ya aiko mana daga Nijar:

A watan da ya gabata ne Muhammadou Issoufou ya lashe zaben shugabancin kasar a karo na biyu.