Boko Haram: Biritaniya za ta tallafa wa Nigeria

An wallafa

Biritaniya ta kudiri niyyar mara wa Najeriya baya wajen yaki da Boko Haram, da kuma taimaka wa da neman yaran da kungiyar ta sace.

A ranar alhini zagayowar shekara biyu da sacewar 'yan matan makarantar Chibok ne, ministan harkokin nahiyar Afrika na Biritaniya, James Duddridge da kuma ministan cigaban kasashen waje Nick Hurd suka fitar da sanarwar hadin gwiwa.

Sanarwar da ke cewa, "'Yan matan Chibok da iyalansu na cikin ranmu, tare da dubban mata da maza da yara kanana da Boko Haram din suka sace."

Sanarwar ta kara da cewa, "Sace yaran nan da aka yi, babban misalin ne na ire-iren ta'asar da Boko Haram din ke aikatawa, zamu kuma tsaya tsayin daka da Najeriya, a yakin da take yi da Boko Haram."

Sun kuma bayyana cewa tun shekarar 2014 ne suka kara dakarun soji da kuma jami'an sirri a kasar domin tallafa wa Najeriya.

Hukumar raya kasashe masu tasowa ta Biritaniya, DFID, ta soma tallafawa gwamnatin kasar ta hanyar kai daukin ababan karatu da kwararrun malamai ga yara kusan 90,000 da suka rasa muhallansu.