Jami'ar Fort Hare ta cika shekaru 100

Asalin hoton, AFP
An wallafa
Jami'ar Fort Hare inda Nelson Mandela ya yi karatu ta cika shekaru 100 da kafawa.
Yawancin jiga-jigan yaƙi da mulkin wariya sun yi karatu a jami'ar ta Fort Hare.
Yayin bukukuwan cikar jami'ar shekaru 100, shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe, wanda tsohon ɗalibin jami'ar ne, ya gabatar da jawabi.
Ɗaruruwan ɗalibai ne dai suka yi yunƙurin kawo cikas ga bukukuwan, amma 'yan sanda suka katse musu hanzari.
Ɗaliban dai suna kira ne a sama musu abinci, da hanyoyin sufuri, da kuma kudaden alawus.
A littafin tarihinsa da ya rubuta marigayi Nelson Mandela ya bayyana jami'ar cewar, tamkar a dunƙule jami'oin Oxford, da Harvard da Yale ne a wuri guda.



























