Moise zai koma Italiya, Arsenal ta gaza dauko Omari Forson

Everton Moise Kean
Bayanan hoto, Dan wasan Everton Moise Kean
An wallafa

Ana hasashen cewa dan wasan Everton Moise Kean, mai shekara 20, zai koma Napoli. Mai yiwuwa Everton ta hukunta dan wasan na kasar Italiya saboda karya dokar hana fita kan cutar korona a farkon makon nan. (Corriere dello Sport - in Italian)

Barcelona ta mayar da hankali wurin sanya dan wasan Brazil Philippe Coutinho, 27, da kuma takwaransa na Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 22, a kasuwa a bazara. (Telegraph)

Chelsea ta so dauko Coutinho amma yanzu ta mayar da hankali wajen dauko dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Kai Havertz, mai shekara 20. (Athletic)

Arsenal ta taya dan wasan Atletico Madrid da Ghana Thomas Partey, mai shekara 26, a kan £43m. (Express)

Liverpool ce a kan gaba wajen yunkurin dauko dan wasan Lille Victor Osimhen, mai shekara 21, ko da yake Leicester da Chelsea suna son dauko dan wasan na Najeriya. (Le Foot Mercato - in French)

Daraktan wasannin Borussia Dortmund ya ce "hankalinsa a kwance yake" game da makomar Jadon Sancho. Ana rade radin dan wasan na Ingila, mai shekara 20, zai koma Manchester United. (Sport1 - in German)

A gefe guda, a shirye Manchester United take ta sayar da dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 27, da dan wasan Ingila Jesse Lingard, mai shekara 27, domin samun kudin sayo Sancho. (Sun)

Arsenal ta gaza dauko dan wasan Manchester United mai shekara 15 Omari Forson. (Mail)

Ana hasashen cewa Manchester United za ta dauko dan wasan Real Valladolid dan kasar Ghana Mohammed Salisu, mai shekara 21. (AS - in Spanish)

Dan wasan Leicester Wilfred Ndidi ya ce yana jin dadin zamansa a kungiyar, duk da tsegumin da ake yi cewa dan wasan na Najeriya, mai shekara 23, zai koma Manchester United or Arsenal. (Teamtalk)

Dan wasan Spaniya Dani Ceballos, mai shekara 23, ya ce yana fatan komawa Real Madrid idan ya kammala zaman aro a Arsenal. (Movistar - in Spanish)

Dan wasan Atletico Madrid Diego Costa ya ce tsohon kocinsa a Chelsea Antonio Conte "ba zai tana" yin karkon zaman kakar wasa guda ba a kungiya irin Real Madrid. Tun watan Mayun 2019 Conte yake jagorantar Inter Milan. (ESPN)

Tsohon kocin Tottenham da Chelsea Andre Villas-Boas ya ce har abada ba zai koma Premier League ba. (Mail)