Goerge Floyd: Shin ya kamata Turawa su biya bakar fata diyya kan bautar da su?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Maya Moretta ta san dangantakar Jami'ar Georgetown da batun bayi lokacin da ta shiga wata makarantar domin yi nazari game da bakaken fata a Amurka.
Sai dai wannan matashiyar 'yar shekara 21 ba ta shirya ganin irin yadda aka yi cinikin bayi ba a dakin karatu na jami'ar. Wani bangare ne na karatunta.
"Wani abu da ya firgita ni shi ne yadda aka rika wulakanta bayi tamkar wasu dabbobi. Na ga takardun da suke bayanin cewa dalibai su kawo barorinsu jami'a a matsayin hanyar biyan kudin makaranta amma kadan.
"Na fahimci abubuwa da dama. Ina jin ya kamata a yi wani abu don gyara rashin adalcin da aka yi a baya," in ji ta.
Daga bisani Maya ta shiga cikin masu muhawara game da batun mayar da bayi wurarensu na asali. Akwai bukatar wanzar da adalci wanda zai magance bukatar gyara tattalin arziki saboda rashin adalcin da aka yi a baya.

Asalin hoton, Courtesy of Maya Moretta
Tunani ne dazai haifar rarrabuwar kai, kamar yadda dalibar da kanta ta gano lokacin da ta fara kamfen a jami'a Georgetown.
"Wasu daga cikin abokaina na suna adawa da daukar kowanne irin mataki, duk da cewa muna da zuri'ar bayi na Georgetown da ke karatu a halin yanzu," kamar yadda ta shaida wa BBC.
Wannan muhawarar wani sabon abu ne. Amma an sake farfado da zanga-zangar 'yancin babaken fata da ake yi wa lakabi da Black Lives Matters a Amurka da kuma wasu kasashe musamman bayan da aka rusa wasu gumaka da suke da alaka da tsofaffin bayi.
Wasu hukumomi da sauran harkokin kasuwanaci sun nemi afuwa saboda rawar da suka taka a cinikin bayi.

Asalin hoton, Getty Images
Daga cikin su akwai babbar majami'ar Ingila da Lloyd's na London, tun karni na uku suke bayar da inshora masu mallakar bayi don gudun asarar bayi da kuma jiragen ruwa.
Ko da Majalisar Dinkin Duniya ma da babban kwamishina a hukumar kare hakkin dan adam da kuma tsohon shugaban kasar Chile Michelle Bachelet, duk sun bukaci a sauya irin yadda ake cin zarafi da kuma nunawa bakake wariya tun lokacin mulkin mallaka ta hanyar biyan diyya.
Mece ce hikimar neman biyan diyyar wadanda aka bautar da su?
Magana ta gaskiya batun neman biyan diyya yana daga cikin fafutukar da masu zanga-zangar 'yancin bakaken fata ke yi tun 2016; kazalika 'yan gwagwarmaya da kungiyoyi sun dade suna makamanciyar wannan fafutukar a fadin duniya.
Babbar muhawarar da ake yi ita ce wadanda suka aka tilasta wa yin aikin bauta ya kamata a biya su diyya saboda ci musu zarafi wanda aka shafe shekaru aru-aru kuma hakan ya shafi rayuwarsu ta hanyar saka su ayyukan wahala.
Masu fafutukar sun mayar da hankali ne ga cinikin baya. An yi fatauci da kuma bautar da mutane kimanin miliyan 11 zuwa kasar Amurka wadanda suka kunshi mata da maza da kuma kananan yara a tsakanin karni na 16 zuwa karni na 19.
Muhawarar ta fi karfi a Amurka inda aka tattauna batun biyan diyyar a majalisar dokokin kasar a 1965, da kuma 2019. Kuma zuri'ar wadanda suka yi bauta na zama a cikin mawuyacin hali.

Asalin hoton, Getty Images
To amma wasu 'yan kasar ma sun dauki matakin magance matsalar bautarwa a cikin al'ummarsu.
Abu mafi muhimmanci shi ne yadda al'umma yankin Caribbea suka kafa wata hukuma a 2013 don samar da tsari na ka'ida da shari'a wajen biyan diyyar.
"Lokacin da kasar Haiti ta samu 'yancin kanta daga kasar Faransa a 1804 bayan da aka kawar da cinikin bayi, an tilasta cewa su biya kwatankwacin dalar Amurka Miliyan 21 don kada dakarun Nepoli su sake komawa fagen yaki," in ji marubuci Dimitri Leger dan kasar Haiti
"Kasata Haiti ta biya tsohuwar uwar dakinta wato Faransa wadda ta yi wa mulkin mallaka, kudin a shekarar 1947."

Asalin hoton, Getty Images
Kasar Barazil da ta karbi bayi fiye da miliyan huɗu daga Afirka a cikin ƙarni huɗu, kasar ta kirkiro da hukumar da za ta saka zuri'ar bayi a wani tsarin fansho.
Kasashen Afirka sun yi kira da a biya su diyya, kuma a 1999 an kiyasta nahiyar za ta karbi dala tiriliyan 777 daga hannu kasashen turai da suka yi mata mulkin mallaka.
Kassara tattalin arziki
Yayin da aka haramta cinikin bil'adama sama da shekaru 200 da suka gabata, har yanzu ana ganin tasirin hakan ta fuskar zamantakewar al'umma da kuma tasirin tattalin arziki tun wacan lokacin.
Amurka ta kawar da tsarin bauta a shekarar 1865 bayan alkawarin kadada 40 ga duk ma'aikacin da ya fice.

Asalin hoton, Getty Images
Daya daga cikin muhawarar da kungiyoyi masu fafutukar suka sanya a gaba ita ce irin tasirin da wariyar launin fata ya haifar da rarrabuwar kai da rashin daidaito a tattalin arziki wanda yake bukatar garambawul.
Ga misali iyalai fararen fata a Amurka, sun nunka iyalai bakaken fata sau goma kuma wannan bambancin yana tasiri a fannoni da dama kamar wajen samun gida da kuma ilimi.
A watan Maris na wannan shekarar, Hannah-Jones ta lashe kyautar Pulitzer, wato kyauta da ake bai wa fitattun 'yan jarida bayan da ta yi wani aiki a 1619 wanda aka sanya wa suna da ranar zuwan bayi Amurka na farko daga nahiyar afrika.
Hannah na daya daga cikin muryoyi da yawa da suka yi imani da cewa diyya ita ce kawai hanyar da za a magance wadannan bambance-bambancen.
"Idan rayuwar bakaken fata ta kasance na da mahimmanci ga Amurka, wannan al'umma dole ne ta wuce taken ƙasa da alamun alama. Lokaci ya yi da Amurka za ta biya bashin da ake bin ta", in ji ta.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Lissafawa (da kuma kafa) lissafin
Daya daga cikin abubuwan da aka fi tattauna game da batun biyan diyyar shine wanda yakamata ya biya kudin kuma nawa za a biya.
An yi kira ga 'yan kasuwa, hukumomi da dangin wadanda suka mallaki bayi da su biya diyya, amma a mafi yawan lokuta lamarin yana komawa kangwamnati ne.
A cewar Verena Shepherd, malami a Jami'ar West Indies kuma mataimakin shugaban hukumar Caricom, babbar manufar ita ce tattaunawa tare da tsoffin kasashen da suka mulkin mallaka don samar da tsarin mai kyau a matakin gwamnati

Asalin hoton, Getty Images
To amma yaya za a saka farashi kan tasirin da cinikin bayi ya yi na tsawon lokaci?
Akwai tsammanin samun kudade masu yawa inda kasashen Afrika suka bukaci a biya su tiriliyan 777 a 1999.
Farfesa William Darity, wani masani tattalin arziki ne a jami'ar Duke, yana daya daga cikin shahararrun masana ilimin kimiyya da ke karatu kan biyan diyyar bayi. Ya kiyasta cewa kusan bakaken fata miliyan 30 suna da magabatan bayi wadanda kuma kowannensu zai samu dala dubu 250,000.
Sai dai ko da matsakaicin adadi na tiriliyan goma da wasu ke hankoran a biya su, wanda ya ninka baki dayan kasafin kudin Amurka na shekarar 2020.
"Manufar biyan diyyar ita ce kawo karshen rashin daidaito tsakanin talakawa bakaken fata da fararen fata," kamar yadda Farfesa Darity ya shaida wa BBC.

Asalin hoton, Getty Images
"Bayan kawo karshen bautar da mutane, lokacin da iyalan bakaken fata suka sami nasara a wasu fanonin rayuwa da kuma arziki, an tarwatsa al'ummominsu ta hanyar kisan gilla ".
An yi lissafin cewa za a iya biyan kusan dala 16,200 kowanne mutum daya.
To ko me wannan kididdigar nufi?
Farfesa Darity ya ce misali kididdiga game da wani fitaccen alkawari na kadada 40 ga kowanne bawa, musamman idan aka yi la'akari da darajar kudi a shekarar 1865 sannan kuma sai a kara kudin ruwa a kai da kuma hauhawar farashin na gwamman shekaru.
A cewar wasu alkaluman kuma sun duba nawa ne za a iya biyan bayi kwatankwacin aikin da suka yi kyauta a baya kyauta.
Sai dai yin hakan ba lallai ba ne saboda lissafin yana da wahala.
'Ajandar biyan diyya'
Magoya bayan biyan diyyar kan bautar da bayi suna fatan cewa abubuwan da ke faruwa na baya-bayan nan dangane da rashin dai daito da kuma cin zarafin da 'yan sanda ke yi a Amurka, lamarin da ya yi mutuwar bakar fatar nan George Floyd a ranar 25 ga Mayu, zai taimakawa wannan fafutukar da suke yi.
Binciken da aka yi kwanan nan a cibiyar Gallup ta buga a bara fito da irin goyon bayan da jama'a ke nuna a fili.
Mafi yawan Amurkawa kashi 67 cikin 100 suna adawa da yunkurin gwamnati da ta ce zata biya kudin ga zuri'ar bayi hannu-da-hannu, kuma wannan adadin na masu adawa da wannan matakin ya karu zuwa kashi 81 cikiin 100 tun a 2002.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images



























