Gudunmawar da babban limamin Ghana ya bayar domin gina coci ta bar baya da kura

Tallafin da babban malamin addinin Musuluncin na kasar Ghana, Dr Osman Nuhu Sharubutu, ya bayar na dala dubu 10 domin gina babbar coci ya bar baya da kura.
Al'amarin ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin Musulmin kasar inda wasu sun marawa limamin limamai kasar baya yayin da wasu kuwa sun nuna rashin jin dadinsu.
Wasu daga cikin masu adawa da matakin sun ce akwai Musulmi da dama a cikin Zangwannin kasar da ke matukar bukatar tallafi irin wannan.
"Muna nan Ghana Musulmi suka ce za su gina masallaci, aka zo ana neman gudunmawar gina wannan masallaci, Kiristoci 'yan uwanmu ba su goyi bayanmu ba, sai da wata kungiya mai zaman kanta ta kasar Tukiya ta zo ta gina mana masallacin," n ji wata mata da ke zama a wani Zango da ke kasar,
Sai dai mai magana da yawun limamin limaman kasar, Sheik Armiyau Shu'aibu ya kare matakin da mai gidan nasa ya dauka, yana mai cewa ya yi haka ne domin kyautata zamantakewa tsakanin al'ummar Musulmi da Kirista.
Ya kuma ce wadanda ka dorawa alhakin gina katafaren coci ne suka kai wa Malam Sharubutu ziyara ta ban girma inda suka sanar da shi irin tanadin da suka yi wajen gina mujami'ar.
"Abin da malam ya yi shi ne ya nuna musu karamci cewa ya ji dadi kuma ga irin na shi gudummuwa da zai bayar, kuma ya yi haka ne don ya karfafa zamantakewa tsakanin musulmi da kirista," a cewarsa.
Sai dai y a ce malam shi kadai ba zai iya daukar nauyin dukanin bukatun Musulmin kasar ba.
"Malam yana ba da kudin asibitin masu jinya kuma yana ba da tallagi ga dalibai masu neman ilimi."
Kusan kashi 13 na al'ummar Ghana musulmi ne kuma sun fi rinjaye a yankin arewacin kasar da kuma yankin gabashin kasar wato Upper East Region.



























