Chelsea da Real Madrid sun tattauna kan Hazard

Eden Hazard
Bayanan hoto, Eden Hazard
An wallafa

Chelsea da Real Madrid sun yi wata ƙwarywa-ƙwaryar tattaunawa kan batun sayen ɗan wasan Belgium mai shekara 30 Eden Hazard - sai dai ƙungiyar ta Sifaniya na son a ba ta ɗan bayan Ingila mai shekara 22, Reece James a maimakonsa. (El Nacional - in Catalan)

Liverpool na sa ido ƙwarai kan Ousmane Dembele a Barcelona. Kwantiragin ɗan wasan Faransar mai shekara 24 ta ƙare, inda kuma bai taka leda ba tun bayan gasar Euro 2020 sakamakon raunin da ya samu a gwiwa a ƙarshen kakar da ta gabata. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Tsohon kocin Borussia Dortmund, Lucien Favre mai shekara 63 da kuma tsohon kocin Chelsea Frank Lampard mai shekara 43 na daga cikin mutum biyu da ƙungiyar Newcastle ke tunanin zaɓa domin maye gurbin Steve Bruce a St James' Park. (Telegraph - subscription required)

Ɗan wasan gaban Arsenal da Faransa mai shekara 30 Alexandre Lacazette ba shi da niyyar sake sa hannu a sabuwar kwantiragi da Gunners idan kwantiraginsa ta ƙare a ƙarshen kakar nan. (Football.London)

Ɗan wasan tsakiyan Wales, Aaron Ramsey mai shekara 30, na da yaƙinin cewa zai taɓuka abin a zo a gani a Juventus ganin cewa yana da kusan kaka ɗaya da rabi a kwantiraginsa. (Times - subscription required)

Georginio Wijnaldum
Bayanan hoto, Georginio Wijnaldum

Ɗan wasan tsakiyar Netherlands Georginio Wijnaldum mai shekara 30 ya ce kwata-kwata ba ya jin daɗin Paris St-Germain - watanni hudu bayan ya je kulob ɗin daga Liverpool. (Independent)

Feyenoord na shirin cinikin ɗan wasan Manchester United da Ivory Coast Amad Diallo mai shekara 19 bayan raunin da ya samu ya kawo cikas a aron da za a bayar da shi a kaka mai zuwa. (Sun)

Manchester United na shawarar sayar da ɗan wasan Ingila Jesse Lingard mai shekara 28 kan fam miliyan 15 a Janairu idan ɗan wasan bai saka hannu a sabuwar kwantiragi ba a Old Trafford inda kwantiragin tasa za ta ƙare a kaka mai zuwa., (Sun)

Real Madrid na son sayen ɗan wasan bayan Sifaniya Sergio Reguilon daga Tottenham Hotspur, sai dai ba su so su biya fam miliyan 39.9 kan ɗan wasan mai shekara 24. (Defensa Central - in Spanish)

Donny van de Beek
Bayanan hoto, Donny van de Beek

Juventus sun soma tattaunawa da Agent din ɗan wasan Manchester United mai shekara 24, Donny van de Beek inda ake son ya koma kulob ɗin a Janairu mai zuwa. (La Stampa via Football Italia)

Juventus ɗin kuma na shirin karɓar aron ɗan wasan Manchester City da Portugal mai shekara 27, Bernado Silva. (Calciomercato - in Italian)

Ɗan wasan Ingila mai shekara 26, Ben Davies na da yaƙinin cewa yana da sauran taka leda a Liverpool duk da ya je kulob ɗin a watan Fabrairu inda daga nan ya tafi aro zuwa Sheffield United. (Liverpool Echo)

Golan Sifaniya David Raya mai shekara 26 ya ce yana jin daɗin zamansa a Brentford duk da Arsenal da Everton sun nuna suna son sa. (Cadena Ser - in Spanish)