Fasahar 5G: Abin da zai sa sabbin wayoyinku su iya kawo cikas ga jiragen sama

.
An wallafa

Manyan kamfanonin jiragen sama na Amurka na gargaɗin cewa fitar da fasahar 5G da ake yi a ƙasashe zai iya jawo bala'i.

Sun bayyana cewa sabuwar fasahar za ta iya jawowa a samu jinkiri wajen tashin jiragen sama, haka kuma zai iya jawowa jirage da dama su kasa tashi kuma babu ranar tashinsu.

Ta yaya fasahar 5G za ta kawo cikas ga sufurin jiragen sama

Abu ne mai tsanani. A ƙarshen 2020, RCTA, wadda ƙungiya ce da ke Amurka, ta fitar da ƙa'idojin da ya kamata a bi kan sufurin jiragen sama - ƙungiyar ta wallafa wani rahoto kan wannan lamari.

Ƙungiyar ta bayyana cewa akwai yiwuwar lamarin zai yi tasiri ga ɓangaren jiragen sama a Amurka, ciki har da matsalolin da za a iya fuskanta da za su iya jawo asarar rayuka da dama, idan aka kasa shawo kan matsalar.

A ƴan kwanakin nan, hukumar da ke sa ido kan sufurin jiragen sama ta FAA ta yi gargaɗin cewa 5G za ta iya jawo matsaloli da dama ga na'urori daban-daban a jirgin sama samfarin 787 Dreamliner.

Hakan zai iya jawo wa jirgin ya kasa rage gudu a wajen sauka, kuma hakan zai iya ja ya wajen sauka ya gusa daga titin jirgi.

Ta yaya za a tafiyar da jirgi cikin kwanciyar hankali

Ba za a bar jirage su yi amfani da na'urar auna nisan jirgi daga sararin samaniya zuwa ƙasa ba a lokutan da za a iya samun cikas ga hanyoyin sadarwar jirgin.

Amma hakan zai iya kawo cikas ga yadda wasu jiragen za su sauka, misali a lokacin da yanayin gari yake dishi-dishi.

Kamfanonin jiragen saman Amurka goma sun yi gargaɗin cewa wannan lamarin zai iya ja jiragen sama da dubu ɗaya su samu jinkiri ko kuma a soke su idan akwai yanayi mara kyau.

..

Shin wasu ƙasashen da ke amfani da fasahar 5G suna irin wannan ƙorafin?

Ba kamar yadda ƙasashen Amurka suke yi ba. Hakan na faruwa ne sakamakon yadda ake ƙaddamar da fasahar 5G ya bambanta a kowace ƙasa.

A Tarayyar Turai, alal misali, kamfanonin sadarwa na aiki ne da zango mafi ƙanƙanta idan aka kwatanta da wanda kamfanonin Amurka ke shirin amfani da su - wanda hakan zai rage yiwuwar samun cikas wajen sadarwa. Haka kuma turakun watsa sabis su ma suna amfani da makamashi kaɗan.

A ƙasar Faransa, akwai wasu yankuna kusa da filayen jirgin sama waɗanda aka haramta amfani da fasahar 5G, haka kuma za a rage tsawon turakun sadarwa domin rage yiwuwar kawo cikas wajen sardarwa.

Sai kuma me gwamnatin Amurka ke yi kan 5G ɗin?

Tuni hukumomi a Amurka suka ɗauki matakai daban-daban.

Hukumar ta ayyana wasu wurare na wucin gadi guda 50 a kusa da filin jirgi, inda masu fasahar za su rage ƙarfin 5G ɗin. Sai dai waɗannan wuraren ba su da yawa idan aka kwatanta da wuraren da ake amfani da su a Faransa inda kamfanonin sadarwar Amurka za su watsa 5G ɗin ta hanyar amfani da makamashi mai yawa.

Haka kuma an sanar da filayen jirgin da za su iya amfani da manhajar GPS domin nuna hanya a maimakon na'urar nuna nisa tsakanin sararin samaniya zuwa ƙasa.

Sai dai kamfanonin jirgin sun kafe kan cewa hakan bai isa ba: sun kafe kan cewa bai kamata a samar da 5G ba a duk wuri da ke da nisan mil biyu daga filin jirgi.

Me kamfanonin sadarwar ke cewa?

Kamfanonin sadarwa na Verizon da AT&T sun dakatar da fitar da fasahar 5G sau biyu haka kuma sun amince da wuraren da aka ayyana da su rage ƙarfin 5G a can.

.