Yadda jiragen saman Najeriya suka kashe Jagoran ISWAP

Sani Shuwaram
Bayanan hoto, Sani Shuwaram
An wallafa

Rahotanni sun ce mai yiwuwa an kashe jagoran kungiyar ISWAP na yankin yammacin Afirka, Sani Shuwaram.

Rahotannin sun ce Shuwaram da wasu mayakan kungiyar sun rasa rayukansu ne sanadin wani hari ta sama a yankin Marte na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Kafar yada labarai ta PRNigeria ta bayyana cewa jiragen saman Najeriya ciiki har da super Tucano sun yi luguden bama bamai a yankin da Shuwuram ya kafa sansani

Rahotanni sun ce Shuwaram ya mutu ne sakamakon harbin bindiga da ya samu a lokacin da jiragen yakin suka kai farmaki sansanin ISWAP da ke yankin Sabon Tumbuns na tafkin Chadi a watan jiya.

Kafar ta PRNigeria ta ce wata majiyar tsaro ce ta tabbatar mata da kisan Shuwaram.

"Shuwaram yana daga cikin 'yan ta'adda da rundunar sojojin sama ta kai wa hari a Sabon Tumbuns kusa da Kirta Wulgo a watan Fabrairun 2022. Hare-haren da aka kai ta sama daga bisani sun yi sanadin mutuwarsa tare da wasu mayakan ISWAP da ake yi wa jinya ciki har da Abu Ibrahim al-Hashimi al- Kurayshi," in ji majiyar .

Sai dai kafar ta PRNigeria ta ce bayanan da ta samu sun ce an zabi Mallam Bako Gorgore a matsayin sabon shugaban kungiyar ta ISWAP wanda zai maye gurbin Shuwaram.

Amma da aka tuntubi Kakakin rundunar sojin sama, Air Commodore Edward Gabkwet, ya ki tabbatar da mutuwar Shuwaram amma ya ce jiragen saman yakin kasar tare da goyon bayan dakarun kasa sun kai farmaki a Tumbuns da ke kusa da Kirta Wulgo a karamar hukumar Marte.

Ya kuma shaida wa BBC cewa sojojin sun kashe 'yan ta'adda amma ba a tantance ko su wane ne ba.

Ya ce abu ne da ke bukatar a yi bincike kafin a sanar.

A watan Nuwamban shekarar 2021 ne mambobin Majalisar Shura na ISWAP suka nada Shuwaram, mai shekaru 45, a matsayin sabon shugaba kungiyar.