Gane Mini Hanya: Yawan ƴan gudun hijira a Najeriya

Bayanan sautiGane Mini Hanya: Yawan ƴan gudun hijira a Najeriya
An wallafa

Latsa alamar lasifika domin sauraren shirin

Yayin da ake ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan bindiga da ke sanadin karuwar ƴan gudun hijira a arewa maso yammacin Najeriya, hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira ta kasar ta ce tana fadi-tashin inganta rayuwar dubban mabuƙatan da ake samu a kullum.

A cewar hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, yanzu haka waɗanda suka rasa matsugunansu saboda bala’i a Najeriya sun haura mutun miliyan uku.

A filinmu na gane Mini hanya na wannan makon, Jabir Mustapha Sambo ya tattauna da Shugabar hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira da Ci Rani ta Najeriya, Imaan Sulaiman Ibrahim, wadda ta fara da bayyana irin ƙalubalen da ke hana samun ainihin alƙaluman ƴan gudun hijira a lokaci guda.