Kasashen biyu na taka leda ne a rukunin B, kuma za su taka leda ne a garin Ellis Park.
Duk kasar da ta lashe wasan za ta tsallake a rukunin ganin cewa duk sun lashe wasanni farko da suka buga.
Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.
Argentina dai ta doke Najeriya ne da ci daya mai ban haushi, a yayinda ita kuma Koriya ta arewa ta doke Girka da ci biyu da nema.
Argentina dai nada zaranta 'yan wasa kamarsu Gonzalo Higuain da Tervez da kuma Messi, a yayinda Koriya ta arewa na ji da kyaftin dinta da ke takawa kungiyar Manchester United leda. Park Ji Sung.