An sabunta: 26 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 17:23 GMT

Karawa tsakanin Amurka da Ghana

Ghana na neman kafa tarihi a gasar ta bana

Ghana na neman kafa tarihi a gasar ta bana

Wannan ne karo na biyu da Ghana ke halartar zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya a jere bayan da tayi hakan a gasar da ta gabata.

Kuma a wannan karon ma ta halarci matakin ne a matsayin kasa daya tilo daga cikin wakilan Afrika a gasar, bayan da ragowar suka gaza.

Ana saran karawar dai za ta kayatar, ganin yadda kasashen biyu ke da matasan 'yan wasan da ke taka leda a sassa da dama na duniya.

Amurka ce dai ta zamo ta daya a rukunin C, bayan da ta doke Aljeriya a wasan ta na karshe. Yayinda Ghana ta zamo ta biyu a rukunin D a bayan Jamus.

Domin ganin sakamakon wasanni kai tsaye da kuma jadawalin rukunai, kana bukatar ka kunna Javascript dinka.

Ana saran Amurka za ta dogara ne kan Landon Donovan na kungiyar LA Galaxy, wanda kawo yanzu ya zira kwallaye biyu a gasar ta bana.

Yayinda ana ta bangaren Ghana za ta dogara kan Asamoah Gyan, wanda ya zira kwallaye shida daga cikin goman da kasar ta zira a bana.

BBC © 2014BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.