Golan United Van dar Sar na tunanin daina kwallo

van der Sar
Bayanan hoto, Tsohon golan Holland Edwin van der Sar
An wallafa

Watakila golan Manchester United Edwin van der Sar yayi ritaya a karshen kakar wasa ta bana.

Tsohon golan Holland din ya koma Old Trafford ne daga Fulham a shekara ta 2005 kuma zai cika shekaru arba'in a ranar 29 ga wannan watan.

Mai horadda gololi a Manchester United Eric Steele ya bayyana cewar "ina tunanin Ed ya yanke shawarar bana ce karshen shekarar kwallonshi".

Amma duk da haka Steele ya kara da cewar akwai yiwuwar Van der Sar ya cigaba da kwallon bayan karshen kakar wasa ta 2010 zuwa 2011 saboda har yanzu bai daga kofin FA kuma yanason ya lashe.