Ronaldo da Messi na ci gaba da haskakawa

Ronaldo da Messi
Bayanan hoto, Ronaldo da Messi na ruwan kwallaye a La Ligar bana
An wallafa

Ronaldo ya zira kwallaye uku a wasan da Real Madrid ta lallasa Athletic Bilbao da ci 5-1, yayin da Barcelona ta casa Almeria da ci 8-0, inda shi ma Messi ya zira kwallaye uku.

Wannan nasara ta nuna cewa har yanzu Real Madrid na ci gaba da kasancewa kan gaba a tebur da maki 32, yayin da Barca ke biye mata dab-da-dab da maki 31.

Yayin da a bangare guda Ronaldo da Messi ke ci gaba da rige-rigen zira kwallaye a tsakaninsu.

Villarael wacce ke mataki na uku ta tashi canjaras ne tsakanin ta da Valencia wacce ke mataki na hudu.