Anderson ya sabunta kwangilarshi a Manchester United

An wallafa
Dan Brazil me bugawa Manchester United kwallon Anderson ya sabunta yarjejeniyarshi da kungiyar na shekaru hudu da rabi.
Dan shekaru ashirin da biyu wanda ya taho Old trafford daga FC Porto a shekara ta 2007 ya buga wasanni 110 duk da yawan jinya da yake yi.
Sir Alex Ferguson yace"mun yi murna ya kulla sabuwar kwangila damu".
Anderson ya fuskanci matsaloli zuwanshi Old Trafford amma a halin yanzu ya kasance daya daga cikin muhimman 'yan wasa a United.
Anderson yace "wannan ce kungiyar da nafison in bugawa kuma ina godiya ga duk wadanda suka taimaka mana".






















