Chelsea na zawarcin David Liuz daga Benfica

luiz
Bayanan hoto, Dan Brazil David Luiz
An wallafa

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce suna kokarin samun maslaha don kulla yarjejeniya da dan kwallon Benfica David Liuz.

Chelsea ta bada tayin pan miliyan 17 akan dan kwallon Brazil din mai shekaru ashirin da uku, amma sai Benfica taki amincewa a watan Disamba.

Da yake jawabi bayanda Chelsea ta lallasa Bolton daci hudu da nema a ranar Litinin, Ancelotti yace har yanzu ba a cimma matsaya ba tsakanin kungiyoyin biyu.

Ya kara da cewar"shine kadai dan kwallon da muke son saye, amma idan bai yiwu ba, babu komai".

Ita dai Benfica ta saka farashin Liuz akan pan miliyan ashirin da biyar da rabi kuma zai iya buga baya a bangaren hagu ko dama.

Idan har ya koma Chelsea, Liuz zai hade da sauran 'yan uwanshi na Brazil wato Alex da Ramires.