London 2012: West Ham ta samu goyon baya

London 2012: West Ham ta samu goyon baya
Bayanan hoto, Barin wurin tsalle-tsalle ya taka rawa sosai a batun filin wasan na Olympic
An wallafa

BBC ta samu labarin cewa West Ham ta samu goyon bayan shugabannin gasar Olympic ta London 2012 a yunkurinta na mallakar filin wasan.

Shugabannin kamfanin Olympic Park Legacy sun yanke shawarar cewa tayin da West Ham ta yi - na barin wurin tsalle-tsallen da ke filin wasan ya fi na Tottenham armashi.

Za dai a nemi kwamitin gudanarwa na kamfanin OPLC ya goyi bayan lamarin, sannan ya sanar da West Ham a matsayin kungiyar da ta cancanci mallakar filin wasan a ranar Juma'a.

Gwamnati da kuma Magajin garin London ne za su yanke hukuncin karshe, amma ana saran za su goyi bayan shawar ta OPLC.

Sai dai mai magana da yawun OPLC ya ce: "Har yanzu ba a riga an yanke hukunci ba".