Tennis: Kvitova ta doke Kim Clijsters

An wallafa
Sabuwar jagorar 'yar wasan Tennis a duniya bangaren mata Kim Clijsters ta sha kashi da ci 4-6 3-6 a hannun Petra Kvitova a wasan karshe na gasar Paris Open.
Clijsters, wacce ta lashe gasar Australian Open a watan Janairu, ta kasa taka rawa kamar yadda aka yi tsammani.
Wannan shi ne kofi na uku da Kvitova, 'yar shekaru 20, ta lashe a tarihinta.
"Wannan ita ce babbar nasara a rayuwa ta. Ta doke ni a baya sau biyu, don haka ina murna na samu nasara a kanta a wannan karon," a cewar Kvitova.
Clijsters, 'yar shekaru 27, ta ce tana fama da matsalar rashin lafiya: "Ina da matsala a kugu na, amma wannan ba hujja ba ce. Ta cancanci ta yi nasara".






















