Carling Cup babbar nasara ce a rayuwata-McLeish

Alex McLeish
Bayanan hoto, Wannan wasa ba karamin koma baya ba ne ga Arsenal
An wallafa

Kocin Birmingham Alex McLeish ya ce nasarar da kungiyar ta samu a kan Arsenal a wasan karshe na gasar Carling ita ce mafi girma a tarihinsa.

Dan wasan Najeriya Obafemi Martins ne ya zira kwallo a mintin karshe wacce ta bai wa Birmingham damar lashe kofin da ci 2-1.

"Na jinjina wa magoya bayanmu, sun dade suna jiran irin wannan rana," kamar yadda McLeish ya shaida wa BBC.

"A gaskiya ita ce nasara mafi girma da na taba samu a tarihin koci na. Ba karamin kokari ba ne ga karamin kulob kamar namu ya doke Arsenal". Birmingham ce dai ta fara zira kwallo a wasan ta hannun Nikola Zigic amma sai Robin van Persie ya farke ma Arsenal a filin wasa na Wembley wanda ya cika makil.