Tennis: Djokovic ya doke Nadal

Asalin hoton, AFP
Novak Djokovic na ci gaba da haskaka wa a kakar bana bayan da ya doke gwarzon Tennis na duniya Rafael Nadal a wasan karshe na gasar cin kofin Sony Ericsson.
Dan wasan na kasar Serbia, mai shekaru 23, ya lashe wasan ne da ci 4-6 6-3 7-6 (7-4), inda ya lashe gasar Masters a karo na hudu a jere.
Wannan ita ce nasara mafi girma da wani dan wasa ya samu a farkon shekara tun bayan Ivan Lendl wanda ya samu nasara 25 a jere a shekara ta 1986.
Nadal, wanda bai taka wata rawa ta azo a gani ba ya ce: "Ina ganin shi zai zamo na daya a duniya."
Ya kara da cewa: "Tun yanzu ya lashe gasa biyu a jere, kuma manya ciki harda Grand Slam daya."
"A binda ya fito fili shi ne cewa nan da wata daya ko biyu, zai zamo na daya a duniya. Amma dai ban sani ba. Ya danganta da sakamakon wasa na.






















