Tarihin Dan Kwallon Nigeria Victor Moses

Mai shekaru 22 kacal, Victor Moses, na kungiyarsa ta hudu ne. Wannan sauyin –daga Chelsea zuwa Liverpool a matsayin aro – shi ne zakaran gwajin dafin da zai nuna ko zai yi tasiri a duniyar kwallon kafa ko kuma zai kasa kai bantensa.
Dan wasan Najeriyar ya hada dukkan shika-shikan da za su ba shi damar yin cikakken tasiri; akwai gudu, ga idon ganin raga, sannan kuma yana da kwarewar da zai iya buga wasa a gefe ko a tsakiya a matsayin mai jefa kwallo a raga.
Moses ya fara wasa a matakin manya ne a Crystal Palace, inda ya buga daga 2007 zuwa 2010, ya jefa kwallaye 11 a raga a wasanni 58 ga kungiyar ta London kafin komawa Wigan. A shekaru biyun da ya yi da su, ya ci kwallaye takwas a wasanni 74.
A watan Agustan 2012 ne ya koma London bayan da Chelsea ta amince ta saye shi kan fam miliyan 9; sai dai dan wasan gaban kwallo daya kawai ya iya zurawa a raga cikin wasanni 23 da ya bugawa kungiyar ta Stamford Bridge.
Lokacin da Jose Mourinho ya koma kungiyar a karo na biyu a matsayin Manaja, sai ya ajiye Moses a benci.
Ya koma Liverpool a matsayin aro na kakar wasanni guda a Satumba kuma nan take ya yi tasiri inda ya ci kwallo a wasansu na farko da Swansea. Kawo yanzu dai ya bugawa jajayen wasanni shida, abinda ya taimakawa kungiyar rawar gani a bana.
A matakin kasa da kasa kuwa, Moses ya koma Nigeria duk da bugawa Ingila wasa da ya yi a matakin matasa har zuwa gasar ‘yan kasa da shekaru 21. Kuma tuni ya taimakawa Super Eagles ta lashe gasar cin kofin kasashen Afrika a 2013.






















