FA: Everton ta doke Swansea 3-1

Lacina Traore
Bayanan hoto, Kwallon farko a wasan farko da Lacina ya zura a ragar Swansea
An wallafa

Everton ta kai wasan daf dana kusa da karshe bayan data doke Swansea a kofin kalu bale wasannin zagaye na biyar.

Lacina Trore dan kwallon da Everton ta dauko aro daga Monaco ne ya zura kwallon farko cikin sauki da dunduniya a minti na hudu da ya fara bugawa kungiyar wasansa na farko.

Swansea wacce take da sabon koci Garry Monk ta farke kwallonta cikin sauri ba tare da bata lokaci ba ta hannun Jonathan de Guzman da ya zura kwallo da ka.

Everton ta kai hare-hare da dama amma sai da koci Roberto Martinez ya sauya Traore bayan ya gaji, ya sako dan kwallon Scotland Steven Naismith

Nan take Naismith ya samu dama ya zura kwallo ta biyu a ragar Swansea lokacin da Neil Tylor ya maida kwallo gida bisa kuskure a minti na biyar da shigarsa wasa, sannan Ashley Richards ya yi masa keta a da'irar raga, Leighton Baines ya buga ya kuma zura kwallo ta uku a raga.

Martinez ne dai kocin da ya dauki kofin FA a lokacin yana horas da Wigan, yanzu kuma yana fatan lashe kofin da Everton a bana.