An dakatar da Anelka buga wasanni 5

Nicolas Anelka
Bayanan hoto, Dan wasan ya ce nunin da ya yi ba yana nufin goyon bayan 'yan Nazi bane
An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta dakatar da dan kwallon West Brom Nicolas Anelka, buga wasanni biyar sakamakon samunsa da laifin nuni da hannu da aka alakanta da goyon bayan 'yan Nazi.

Haka kuma an ci tarar dan wasan £80,000 da kuma tilasta masa daukar darasi a makaranta.

Anelka ya nuna kasa da hannunsa ne, a sigar da ake dauka koyi da 'yan Nazi masu kin Yahudawa ne, bayan da ya ci kwallo a wasansu da West Ham a gasar Premier ranar 28 ga Disamba.

Kamfanin Zoopla mai daukar nauyin West Brom zai kawo karshen alakarsa da kungiyar a karshen kakar bana saboda nunin na Anelka ya yi.