'Man U ta nuna rashin kwarewa'

David Moyes ya godewa Sir Alex Ferguson
Bayanan hoto, David Moyes ya godewa Sir Alex Ferguson
An wallafa

An zargi Kulab din Manchester United da nuna rashin kwarewa bayan korar David Moyes.

BBC ta fahimci cewa Moyes ya fusata game da yadda kulab din ya kore shi.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba Moyes ya ce yayi alfaharin shugabantar Kulab din, kuma ya godewa Sir Alex Ferguson saboda damar da ya bashi na zama shugaba.

Amma Kungiyar masu horar da wasan Premier League tace kulab din Manchaster United ya nuna rashin kwarewa a matakin da ya dauka.