Brazil: Carrick baya cikin tawagar Ingila

Manajan Ingila zai bayyana 'yan tawagar kasar a yau
Bayanan hoto, Manajan Ingila zai bayyana 'yan tawagar kasar a yau
An wallafa

Dan wasan tsakiyar Manchester United Michael Carrick ba zai kasance cikin tawagar 'yan wasan Ingila a lokacin ba a lokacin da Manajan Ingilan Roy Hodgson zai bayyana wadanda ke ciki a ranar Litinin, kamar yadda BBC ta gano.

Dan wasan mai shekaru 32 kuma tsohon dan wasan West Ham United da kuma Tottenham ya taka wasan da kasar sa ta buga da Poland a cikin watan Oktoba.

Manajan Ingilan mai shekaru 66, zai bayyana sunayen 'yan tawagar a Luton a yau.