World Cup 2022: Turai na son a yi cikin damuna

World Cup 2022
Bayanan hoto, Har yanzu ana takaddamar watannin da za a fara gasar
An wallafa

Manyan kungiyoyin nahiyar Turai za su bukaci FIFA a makon gobe ta dage gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci a 2022 daga ranar 28 ga watan Afirilu.

A 2010 aka bai wa Qatar izinin karbar bakuncin gasar kofin duniyar, sai dai har yanzu ana takaddamar lokacin da ya kamata a yi gasar saboda yanayin zafi a lokacin.

Kungiyar Manyan kulob-kulob din Turai ECA ta kun shi Manchester United da Liverpool da Barcelona da kuma Bayern Munich.

Cikin bukatun da kungiyar za ta nema a wajen FIFA, sun hada da fara kakar wasannin League mako biyu kafin yadda aka saba, da fara gasar FA bayan gasar cin kofin duniya.

Da yake sai a ranar 29 ga watan Mayu ne za a buga wasan karshe na cin kofin duniya, hakan zai shafi gasar Premier da sauran wasannin da za a kammala cikin watan Yuli.

Kungiyar ECA mai wakiltar manyan kungiyoyin kwallon kafa 214, tace gasar kuma za ta kawo tsaiko a kasar Faransa da Spaniya da Jamus.