Balotelli ya ceto Liverpool daga hannun Tottenham

Balotelli ne ya ceto Liverpool daga hannun Tottenham
Bayanan hoto, Balotelli ne ya ceto Liverpool daga hannun Tottenham
An wallafa

Kwallon farko da Mario Balotelli ya zura a gasar Premier ta bana ta bai wa Liverpool nasara a kan Tottenham a fafutikar da suke yi na zama daya daga cikin kulob hudu a saman tebirin gasar.

Kulob din Liverpool ne ke kan gaba da ci 2, sai dai Tottenham sun farke kafin a sanya Balotelli wanda ya maye gurbin Daniel Sturridgee mintuna bakwai kafin a tashi daga wasa.

Nan da nan Balotelli ya samu kwallo ya zura, lamarin da ya sa suka tashi da ci 3-2.

Koda yake Raheem Sterling bai taka leda ba saboda raunin da ya ji, amma Sturridge ya dawo bakin-daga a karon farko tun karawar da Liverpool suka tashi 3-0 a White Hart Lane ranar 31 ga watan Agusta.