Hazard ya tsawaita kwantiraginsa da Chelsea

Asalin hoton, Getty
An wallafa
Eden Hazard ya rattaba hannu kan tsawaita kwantiraginsa da Chelsea na tsawon shekaru biyar da rabi.
Dan kwallon Belgium, mai shekaru 24, ya koma Chelsea ne kan kudi fam miliyan 32 daga Lille ta Faransa a shekarar 2012.
Kuma shi ne dan wasan da aka zaba a Chelsea da ya fi yin fice a gasar Premier bara, ya kuma ci kwallaye 13 a bana daga cikin wasanni 36 da ya buga.
Hazard wanda ya buga wa Belgium gasar kofin duniya a Brazil a bara, ya buga wa Chelsea wasanni 147 ya kuma ci kwallaye 43.



























