An rage hukuncin Nemanja Matic

Asalin hoton, Getty
An rage hukuncin da aka yi wa dan wasan Chelsea Nemanja Matic na dakatarwa daga buga wasanni uku kan jan katin da alkalin wasa ya ba shi lokacin wasanusu da Burnley.
Alkalin wasan ya hukunta shi ne sakamakon bangaje dan wasan Burnley Ashley Barnes da ya yi har kasa, saboda ya yi masa keta.
Kwamitin hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila mai zaman kansa, shi ne ya rage hukuncin daga buga wasanni uku zuwa biyu bayan ya saurari bahasin Chelsea a yayin daukaka karar da ta yi.
Duk da wannan sassauci dan wasan ba zai buga wasan karshe na kofin Capital One ba, da Chelsean za ta yi da Tottenham ranar Lahadi.
Kuma wasan da za su yi da West Ham na Premier ranar Laraba hudu ga watan Maris, shi ma ba zai buga ba.
A wata sanarwa da kungiyar ta Chelsea ta fitar ta ce ba ta ji dadin wannan hukunci ba, na rashin rage hukuncin yadda ya kamata, kamar yadda dokokin hukumar kwallon Ingilan suka tanada.






















