Alves zai sanar da makomarsa a Barcelona

Asalin hoton, getty
An wallafa
Dan kwallon Brazil mai tsaron baya a Barcelona zai sanar da makomarsa a kungiyar bayan kammala Gasar cin kofin Zakarun Turai.
Dan wasan mai shekaru 32, wanda ya yi shekaru bakwai a Barca, an yi rade-radin cewar zai koma Paris St-Germain taka leda, bayan da ya ki tsawaita kwantiraginsa.
Barcelona za ta buga Gasar Kofin Zakarun Turai ranar 6 ga watan Yuni da Juventus, kuma za ta buga wasan karshe a Copa del Rey.
A karshen kakar wasan bana ne kwantiragin Alves zai kare da Barcelona, kuma shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ya ce yana fatan dan wasan zai ci gaba da zama a Nou Camp.
Banda PSG ta Faransa da take zawarcin dan kwallon, an kuma ce watakila Alves ya koma buga gasar Premier kuma da Manchester United.






















