Tottenham ta raba gari da Adebayor

Adebayor ya koma Tottenham taka leda a 2012
Bayanan hoto, Adebayor ya koma Tottenham taka leda a 2012
An wallafa

Tottenham da Emmanuel Adebayor sun amince kan soke yarje-jeniyar da suka kulla a tsakaninsu.

Adebayor mai shekaru 31, bai buga wa Tottenham wasa a bana ba, sannan sunansa baya cikin 'yan wasan da suke buga Premier da wadanda za su buga mata Europa League.

Sauran shekara daya kwantiragin Adebayor wanda aka dauko daga Manchester City a 2012 ya kare da Tottenham.

West Ham da Aston Villa sun yi zawarcin Adebayor kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula, a inda suka yi korafin cewar ba za su iya biyan albashin dan wasan ba.