Za a cigaba da gasar French Ligue 1

A ranar Juma'a a shiga wasannin mako na 14 a gasar ta Faransa
Bayanan hoto, A ranar Juma'a a shiga wasannin mako na 14 a gasar ta Faransa
An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Faransa ta ce za a ci gaba da buga gasar cin kofin kasar a karshen makonnan, duk da harin da aka kai wa kasar a ranar Juma'a.

Sai dai ba za a bar magoya bayan duk kungiyar da za ta je wasa waje ba su bi ta karawar, saboda dalilai na tsaro.

A ranar Juma'a ce aka kai hari a Paris wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 129 ciki har da 'yan kunar bakin wake uku da suka mutu daf da filin da Faransa ke buga wasan sada zumunta da Jamus.

Nice ce za ta karbi bakuncin Olympique Lyonnais a wasan mako na 14 da za a ci gaba a gasar da za su fafata a filin wasa na Allianz Riviera.

Ministan wasannin kasar Faransa ya shaida wa BBC cewar za su karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turai a shekara mai zuwa kamar yadda aka tsara.

Ita ma hukumar kwallon kafa ta Turai ta sanar da cewar babu batun dage gasar da za ayi a shekarar 2016 a Faransa duk da harin da aka kai mata.