Ebola zai dambata da Mai Takwasara

An wallafa

Da yammacin Lahadi ne Ebola da Mai Takwasara za su dambata a wasan damben gargajiya da ake yi a jihar Sokoto, Nigeria.

Tun da yammacin Asabar ‘yan wasan biyu suka so takawa a damben, amma cikar da filin ya yi da shigar ‘yan kallo cikin da’irar fili yasa suka kasa yin fafatawar.

Ebola ya kashe Mai Takwasara a Zaria a cikin watan Fabrairu, saboda haka Mai Takwasara fansar kisan zai nema

Wasu daga cikan wasannin da za a yi Cikan Guramada da Bahagon Balan Gada da kuma wasa tsakanin Shagon Aleka da Hagu na Duten Mari.

Kungiyar damben gargajiya ta Nigeria ce ta hada wasannnin domin farfado da wasan a kasa da duniya.