An cire alkalin wasa saboda Leicester

Alkali Kevin Friend mai goyon bayan kungiyar Leicester ne
Bayanan hoto, Alkali Kevin Friend mai goyon bayan kungiyar Leicester ne
An wallafa

Hukumar gasar Premier ta cire Kevin Friend wanda a da aka tsara zai yi alkalancin wasan Tottenham da Stoke City na ranar Litinin, saboda shi mai goyon bayan kungiyar Leicester ne, wadda ke matsayi na daya a tebur.

Kungiyar Tottenham ita ce ke bin Leicester City a tebur da bambancin maki bakwai tsakaninsu yayin da ya rage wasanni biyar a kammala gasar ta bana.

Hukumar alkalan wasa ta Ingila (PGMOL) ba ta sanya Friend, wanda ke zaune a Leicester, kuma yake zuwa kallon wasansu a matsayin kashin kansa, ya yi alkalancin wasannin kungiyar.

Hukumar ta ce bisa la'akari da lokaci da kuma matsayin wasan ya sa aka sauya shi, a wasan da za a yi na Tottenham da Stoke City.

A madadinsa yanzu an sanya Neil Swarbrick daga Preston ya yi alkalancin wasan a Stoke, shi kuwa Friend din zai kula da wasan Newcastle da Manchester City a ranar Talata.