Yadda Hungary ta ci buri kan yaran da ke tasowa

Jonas Salk ne ya samu nasarar gano allurar rigakafin shan-inna a tsakiyar shekarun 1950 (Science Photo Library)
Bayanan hoto, Jonas Salk ne ya samu nasarar gano allurar rigakafin shan-inna a tsakiyar shekarun 1950
An wallafa

Bayan yaki, kasashen ko'ina sun yi karancin 'yan kadagon da za su yi aikin kyautata rayuwar al'umma - ko da tsarin tattalin arzikinsu na jari hujja ko kwamunisanci ne.

Hungary ta shiga tsaka mai wuya: ba ta da bunkasar masana'antu don haka babu ma'aikatan da za su aikin gina kasar kwamunisanci.

Sai dai al'ummarta da suka rayu bayan yaki suna da karfin yin aiki matukar ba za a tuhumesu a matsayin masu hannu da shuni ko 'yan tada kayar baya ba, wadanda suka yi yaki tare da Jamusawa 'yan Nazi (mabiyan Hitler), ta yadda masu irin wannan manufa aka dauke su abokan gaba.

Lokacin da Birtaniya ke karfafa gwiwar masu son yin kaura daga kasashen da taba yi wa mulkinm mallaka don kara yawan ma'aikatanta, kasar Hungary ta tattara burinta kan kananan yara.

Ta ba su ilimi ingantacce da abinci da kula da lafiya kyauta, ta yadda za su girma su zama masu kwazon aiki, wato masu hakar ma'adanai da masu aikin karfe. "Duk inda ka duba za ka ga hotunan lafiyayyu masu tada kwanji na al'umma masi kwazon aiki.

Ba za ka iya kawar da kai ba. Mutum-mutumi da hotuna da jaridu da mujallu duk suna nuni da irin wanan manufa," in ji Dora.

Don tabbatar da cikar wannan buri, gwamnati ta bullo da matakan karfafa gwiwar mata su haifi 'ya'ya. Ba a ma damu da cewa ko ba su da aure ba.

Farfagandar zaburar da su cewa: "Haihuwa aiki ne da ya rataya kan matan aure, kuma matarba ce ga 'yan mata marasa aure."

A dora harajin musamman ga duk wanda ya kai shekara 20 bai haihu ba. Tun daga 1952 aka mayar da zubar da ciki laifi, tare da gurfanarwa a gaban hukuma (yarda da aikata laifin ma ba ta taso ba) ga matan da ake tuhuma da zubar da ciki da likitocin da suka yi musu aikin.

Don bai wa iyaye mata damar tutiya da jariransu a tituna da dandali-dandalin Hungary, sai kamfanin kera bas na Ikarus ya fara yin kujerun jarirai masu taya a shekarar 1954 - shekarar da Gyorgy ya kamu da cutar shan-inna.

Daya daga cikin mafi soyuwar hotunan da Dora ta gano a lokacin bincikenta na hotunan da aka dauka mafi kyawu a zamanin shi ne kujerar jarirai mai siffar bas (tare da mace tana kalami mai taushi) a gaban layin iyaye masu shiga bas-bas cike da alfahari.

Nazarin shan-inna ya nuna cewa cuta ce da ke far wa yara ta gurgunta su, inda annobarta ta farko ta auku a shekarar 1952, ta biyu kuwa ita ce wadda ta shanye wa Gyorgy kafafu a shekarar 1954.

A shekarar dai kasar Hungary ta sa ido kan yadda aka yi gwajin farko a duniya na rigakafin shan-inna, inda aka farad a yara fiye da miliyan guda a Amurka.

Gwajin allurar Salk ya yi nasara, hart a kai ga an yui mata lakabi da sunansa (Jonas Salk), masanin kimiyya Bayahuden da ya fito daga New York, wanda ya kirkirota ta hanyar amfani da kwayar cutar da ba ta motsi, inda nan da nan aka yadata a fadin Amurka.

A Afrilun 1955 dakin binciken Cutter na Amurka (daya daga cikin kamfanonin da aka bai wa lasisi samar da rigakafin) ya fitar da rukunin farko na kwayar cutar shan-inna mara motsi.

Sanadiyyar hakan kimanin Amurkawa 200 da aka yi wa rigakafin suka kamu da shan-inna. Jaridar Hungary ta yi hanzarin baza cewa, "saboda sakaci dubban yara an mayar da su dabbobin gwajin mummunar kariyar kyauta."

Kungiyar Likitocin Amurka, daga bisani ta dora alhakin 'kazancewar lamarin' kan yawan gwaje-gwajen da aka yi har dakin binciken Cuttter ya yi kaurin suna.'

Kuma a Yunin wata shekarar bayan samun dimbin nasara a duniya sai aka tabbatar da kariya da ingancin rigakafin Salk, inda Hungary ta fara samar da ita a gida.

Ta ma fadada shirin inda ta tura masana kwayoyin cututtuka da Daraktan yin rigakafin cututtukan mutane da cibiyar bincike (kamfanin yin magungunan rigakafi) zuwa kasar Denmark, wata cibiyar binciken cutar shan-inna ta Turai a lokacin..

Ganin an bari sun tsallaka katangar karfe abinj farin ciki ne, bisa la'akari da cewa daukacinsu masana kimiyya ne, wadanda suka hada da likitocin dabbobi da na mutane, wadanda suka zama ja-gaba wajen bai wa al'umma kariyar lafiya kafin yaki.

Amurka ba ta wasarairai da masa kimiyyarta, har ta kai ga ta yi watsi fasfo 600 na neman izini shiga kasar bisa dalilan siyasa kafin shekarar 1958.

Sai dai likitoci dam asana kimiyya sun yi karanci. Mafi yawancinsu sun tsere lokacin da 'yan Nazi suka mamayi Hungary a shekarar 1944.

Wasunsu suka komo daga Rasha a matsayin fursunonin yaki a sansani 'ba za su iya yin aiki ba' (sakamakon tawaya ko azaftarwa) ko an mayar da su kurkukun Saberiya saboda dangantakarsu da masu hannu da shuni. Tsananin bukata dai ya bai wa masana kimiyya 'yancin walwala fiye da malaman jami'a a sauran fannonin ilimi, a cewar Dora.

"Jam'iyya (mai mulki) ta kawar da ido daga manufofinsu na siyasa da akidun zamantakewar rayuwa, kuma bayan wani lokaci sai likitoci da m asana kimiyya suka sake smaun irin matsayin da suke da shi a al'umma kafin yaki. Ba a samu sauyin zamantakewar al'umma yadda take kafin yaki - sai ma sababbin tsare-tsaren rashin daidaito (na adalci).

Watanni hudu sukar lamirin Amurka da Gwamnatin Hungary ta yi sai ya zame mata dole ta amince da cewa ta yi sakaci. Don haka gina sababbin asibitoci ya zama a kan gaba a tsarin gina kasa na shekara biyar, cikin shekarar 1950, an fitar da tsarin tattalin arziki da bunkasa masana'antu.

Amma a ran ar 19 ga Oktobar 1956, Ministan Lafiya Jozsef Roman ya sanar da shugabannin cibiyoyin kula da lafiya cewa babu wadda aka gina. Asibitocin da ake da su a cunkushe suke, don shawo kan matsalar sauran gine-ginen daba a yi su da nufin kula da lafiya ba, an mayar da su kananan asibitoci (an fara kafa ORFI a tsohon otal).

Roman ya yi ikrarin cewa an yi wasarairai da cibiyoyin kula da lafiyar al'umma da na hana yaduwar annoba.

Jaridun duniya sun yada nasarar da rigakafin shan-inna na Salk ya samu (March of Dimes/Wikimedia Commons)
Bayanan hoto, Jaridun duniya sun yada nasarar da rigakafin shan-inna na Salk ya samu

Rashin zuba kudi a harkar kula da lafiya wauta ce, musamman tun da kula da lafiya kyauta babban jigo ne da shugabannin 'yan kwamunisanci ke amfani da shi wajen fifita kimar darajar tsarinsu a kan jari hujjan Yammacin Turai, tattare da nuna cewa lafiyayyen jiki ke samar lafiyayyar kwakwalwa da za ta zabar muku mafificiyar akidar rayuwa.

"A dan takaitaccen lokaci rahotanni jarida sun kwata bankado maganganun mista daga kundin tarihi," in ji Dora.

Kakanninta sun tabbatar da gaskiya. Asibitin da aka duba Gyorgy a Debreceen ya nuna gazawa wajen kula da dimbin yaran da ke fama da cutar shan-inna.

Jami'an kula da lafiya da Janos ke hulda da su sun ba shi shawara kan cewa ORFI na babban wurin kula da masu fama da cutar shan-inna, sannan suna da managartan kayan aikin gyaran gabobin da cutar shan-inna ta lauye, don haka ioyalan Vargha suka mayar da dansu zuwa Budapest kimanin kilomita 250 daga inda suke zaune.

Lokacin yana dan shekara uku, Gyorgy yanzu al'amura kadan zai iya tunawa da suka faru a loakacin da ya shafe a garin Debrecen, in da ya yi fama da ciwon laka (aka rika tsira masa allura a jijiya.

Kuma har farkon shekarun 1950 an a ganin aikin a matsayin tsohuwar dabnarar da aka daina aiki d aita, saboda zafinta, wajen tarairayar cutar shan-inna).

"Na tuna na yi rubda ciki kan teburin aiki, ina kukan zafin ciwo," in ji shi. "Kuma na yi rigingine a kan gado, wanda ke karshen sakon dakin asibitin, inda ta yiwu muna tare da kimanin yara 12. Da malamar jinya ta zo gadona sai na fara kuka kafin ta iso kaina."