Yadda al'umma mai zuwa za ta soki lamirinmu

Nuna wariya
An wallafa

Na yi wata tattaunawa inda na yi wata tambaya mai tayar da hankali cewa: Yaya za a kalle ni bayan na mutu?

Ina sha'awar yin tunanin kaina a matsayin mai tarbiyya da kwazon aiki da kyakkyawar dabi'a.

Sai dai ta yiwu ba za a dauka haka ba a kodayaushe.

Ta yiwu ma babu wani a cikinmu da zai kasance hakan.

Kowace irin kyakkyawar niyya da tausasawa da kake da ita, abin da muka dauka mai kyau daidai ko yardajje a al'umma na iya sauyawa.

Tun daga kan bauta zuwa nuna fifikon jinsi, akwai dimbin abubuwan da muka kyama dangane da dabi'un rayuwa.

Duk da haka ya yin da kowace al'umma ke yaba wa kanta kan yadda ta fito daga kungurmin duhun zamanin iyaye da kakanni irin wannan kawai gurgun tunani ne.

Na yi ta musayar dabaru kan lamarin tsakanina da Tom Standage, wani marubuci kuma editan al'amuran da suka shafi na'ura mai kwakwalwa a mujallar The Economics.

Mun fara ne daga kan mashahuran shirye-shiryen da ake gabatarwa a talabijin tun daga shekarun 1970 wadanda ke damfare da ra'ayoyi da kalaman da ake ganin baikensu, ta yadda ba za a iya amfani da su wajen watsa shirye-shirye a yau ba.

Sai dai a cewarsa: "Ko lamarin zai kasance da sauki mu yaba wa kanmu kan yadda ba za mu kasance masu son rai fiye da al'ummomin da suka gabata ba."

Irin wannan gurgun tunanin na da hadarin sanya jiji da kai.

Zai iya zama hanyar yaba wa kanmu kan ci gaban da aka samu fiye kokarin ganin dorewarsa, tare da kawar da kai daga matsalolin da ke tattare da halin da muke ciki.

Karin abin sha'awar shi ne, muna jin irin wannan tambayar: yaya al'ummarmu za a dubeta a baya?

Yaya jikokinmu za su ga baikenmu kan al'amuran da muka dauka sakaka (da sauki)?

Nuna wariya cikin shekarun 1950 ya yi muni a yau, amma shin mun samu hakikanin ci gaba?

Wasu al'amuran yiwuwarsu karara take, a bayyane fiye da wasu cin nama da noman zamani (ta hanyar amfani da na'urori) ta yiwu a ce al'amura ne da ke tabbatar da yarda, bisa la'akari da amfani da dimbin albarkatu tattare da munanan al'amuran da take nuni da su.

Abin da wani almubazzarancin da masu zuwa nan gaba za su yi takaicinsa shi ne yawan amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta (Antibiotics).

Dangane da rashin adalcin son rai kuwa, al'ummar da ke biye mana akwai tabbacin cewa za su cika da mamakin yadda aka tauye wani rukuni na mutane kamar mata-maza wadanda ake nuna wa kyara.

Baya ga yadda a wasu sassa na duniya ake daukar masu auren jinsi da aikata miyagun laifuka, tare da tauye hakkin mata, ko kuma yadda aka dauki wani rukuni na ma'aikata tamfar bayin zamani.

Daukacin wadannan al'amura su ne hakikanin abubuwan da ya kamata a ce mun shawo kan su yanzu nan take; kan al'amuran da muke burin ganin sun tabbata, da kuma irin duniyar da muke fatan bar wa na baya gado.

Abin da ya fi ba ni mamaki, ko mene ne manyan masu juya akalar tunanin al'ummar duniya za su zakulo daga tambayata?

Ko al'ummar da za ta biyo bayanmu za ta kyamaci kibarmu?
Bayanan hoto, Ko al'ummar da za ta biyo bayanmu za ta kyamaci kibarmu?

Tun da kula da muhalli ta yiwu a ce shi ne muhimmin gadon da za mu bar wa 'ya'yanmu, sai na gabatar da al'amarin ga jigon da ya kafa dabarun kula da muhalli na zamani mafi tasiri.

James Lovelock, masanin kimiyya dan Birtaniya wanda ya bullo da mahangar Gaia.

Ya kasance mutum na farko da ya kamata a tuntuba saboda mahangar dabararsa ta wadda ta yi nuni da cewa duniya kanta za a iya kallon ta a matsayin wani tsarin daidaituwar al'amura na kashin kai, don haka sauye-sauyen da dan Adam ya kawo zai haifar da wasu al'amura da ke da karfin tarairayar rayuwa da ci gaban al'umma kamar yadda muka sani.

Lovelock wanda aka haife a shekarar 1919 tuni ya ga juyi iri-iri a duniya game da zamantakewa fiye da mafi yawanmu.

Da yake amsa tambayata, sai ya ce ra'ayinsa na kashin kansa, bisa la'akari da yadda 'ya'yansa za su dubi baya kan halin yanzu da hangen shekaru masu zuwa.

"'Ya'yana hudu da jikoki tara da tattaba kunne bakwai," inji shi.

"Ina jin cewa na cancanci in amsa tambayar."

Hakikanin jikokinsa, a cewarsa, ba sa takaicin halin da muke ciki a yanzu tamkar yadda ake zata.

"Sun dauki wannan zamani sakaka kawai, kuma takaicinsu kawai bai wuce al'amuran da suka shafi yake-yaken kabilanci ba."

Al'ummar da ba ta zo duniya ba, ita ce za ta rudu da illar almubazzarancin da aka yi a muhalli.

"Har yanzu muna samar da abubuwa," kamar yadda Lovelock ya fada mini.

"Ina jin cewa 'ya'yana da aka haife su kwananan nan da shekara ko fiye za su fara jin takaicin gazawar gwamnatocinmu (ba tare da la'akari da yanayin siyasa ba) wajen bayar da kariya (ga Birtaniya) ta zama muhallin zama mai kyau."

Ya ci gaba da cewa: "Ko mun manta da cewa yunwa ta kusa kashe mu a lokacin Yakin Duniya na Biyu?"

"Muna bukatar makamashi don mu rayu.." da kuma cewa kowane al'amarin da ya shafemu a yau na jin dadi da ci gaba ba shi da tabbas.

.. sakacinmu wajen kasa rage iskar gas da ake bulbula wa tsirrai?

A wajen mutane da dama da na sani, akwai wani abu da ke kawo tarnaki game da sauyin yanayi: abin tsoron da ake tababarsa.

Duk da haka jikokinmu za su ji shi daban, kamar yadda wani kwararren da na gana da shi ya yi takaddama akai, wato Kate Raworth, masaniyar tsimi da tanadi a cibiyar nazarin sauyin muhalli ta Jami'ar Oxford.

Raworth na da tabbacin cewa 'ya'yanmu za su yi "tur da tsarin tunaninmu na jajircewa kan manufa ta kai-tsaye."

A iya cewa hanyar da muke bi wajen warware matsaloli kamar tunkarar sauyin yanayi a kebe.

Tsawon zamani an samu tunani na daban wajen bibiyar al'amuran duniya bisa tafarkin "tsararrun tunane-tunane" da za su bayyana.

Wannan matsalar na nufin, a cewarta, muna daukar fannoni kamar ilimi da bunkasar tattalin arziki da kula da muhalli tamkar ba su da alaka, alhali alakarsu sargafe take da juna kawai da a ce ba mu samu cikakkiyar fahimta ba, zuwa yanzu.

"Tattalin arziki yana kunshe ne cikin al'umma, wadda ke zaune a duniya, kuma daukacin wadanan tsare-tsare duk suna cudanya da juna."

… dogaronmu na gurbata iska na tafiya?

Akwai tabbbaci daga hasashen Lovelock.

Nan gaba al'umma za su samu kyakkyawar fahimtar yadda duniya ke juya akalar al'amuranta da kuma yadda harkokin da muke gudanarwa ke barazana ga kwanciyar hankalinmu, sannan yadda ya kamata tsarin tattalinmu ya sake mahangar nazari, cewar Raworth.

Wannan hikimar za ta kawo kyakkyawan sauyi a tsarin rayuwarmu kan yadda za mu rika tunanin duniyarmu.