Griezmann ba zai buga karawa da Real ba

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Watakila dan wasan Atletico Madrid, Antoine Griezmann, ba zai buga karawar da kungiyar za ta yi da Real Madrid a ranar Asabar, sakamakon raunin da ya yi.
Griezmann ya yi rauni ne a fafatawar da Faransa ta ci Sweden 2-1 a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka yi a ranar Juma'a.
Tuni dan kwallon ya koma Spaniya domin yin magani, kuma hakan na nufin ba zai buga wasan sada zumunta da Faransa za ta yi da Ivory Coast ba a ranar Talata.
Atletico ce za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan hamayya a gasar cin kofin La Liga wasannin mako na 12 a ranar Asabar.
Griezmann mai shekara 25, shi ne dan wasan Atletico da ya fi yawan ci wa kungiyar kwallaye a kakar bana, inda ya ci guda shida.























