An dage karawa tsakanin Madrid da Valencia

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Hukumar kwallon kafa ta Spaniya ta dage wasan cin kofin La Liga tsakanin Real Madrid da Valencia wanda aka tsara za su kara a ranar 18 ga watan Disamba.
An dage karawar ne saboda da Madrid za ta buga wasan gasar cin kofin zakarun nahiyoyi da za a yi a cikin watan Disamba, inda za ta wakilci nahiyar Turai, bayan da ta ci kofin zakaru na 11 na Turai a tarihi.
Tun farko an tsara cewar Real Madrid za ta ziyarci Valencia a wasannin mako na 16 a gasar cin kofin La Liga a ranar Lahadi 18 ga watan Disamba, amma an dage wasan zuwa wani lokaci.
Madrid wadda ta lashe kofin duniya na zakarun nahiyoyi a shekarar 2014, tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 27, yayin da Valencia ke matsayi na 15 da maki 10.























