Keane na Hull zai yi jinyar shekara daya

Asalin hoton, Rex Features
An wallafa
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Hull City, Will Keane, zai yi jinyar shekara daya, sakamakon raunin da ya yi a gwiwarsa.
Keane mai shekara 23, ya yi rauni ne a karawar da kungiyarsa ta ci Southampton a ranar 6 ga watan Nuwamba.
Dan kwallon ya koma Hull City da murza-leda daga Manchester United a ranar 30 ga watan Agusta, kuma tuni ya yi wasanni shida a kungiyar.
Keane ya taba yin doguwar jinya a shekarar 2012 a rauni iri daya da wanda ya yi a yanzu a lokacin da yake taka-leda a matasan tawagar kwallon kafa ta Ingila masu shekara 19.
Hull City tana mataki na 18 a kan teburin Premier.























