Zakarun Turai: An kammala wasannin rukuni

Asalin hoton, EPA
An kammala sauran wasannin rukunan gasar Zakarun Turai inda aka samu ragowar kungiyoyi takwas da su ka cika 16 da za su yi wasan zagaye na gaba na sili-daya-kwale.
Ga sakamakon wasannin:
Bayer Leverkusen 3-0 Monaco; Tottenham 3-1 CSKA Moscow; Real Madrid 2-2 Borussia Dortmund
Legia Warszawa 1-0 Sporting CP; Club Brugge 0-2 Kobenhavn; Porto 5-0 Leicester City
Lyon 0-0 Sevilla; Juventus 2-0 Dinamo Zagreb
Ga kungiyoyi takwas din da suka yi nasarar tsallakewa:
Group E: Monaco ta daya da maki 11, sai Bayern Leverkusen ta biyu da maki 10, amma Tottenham ta samu gurbin gasar zakarun Turai ta Europa da maki 7.
Group F: Borussia Dortmund ta daya da maki 14, sai Real Madrid ta biyu da maki 12
Group G: Leicester ta daya da maki 13, sai FC Porto da maki 11
Group H : Juventus ta daya da maki 13, sai Sevilla da maki 11
Ga jerin wadanda suka yi na daya a rukuni-rukuni
Arsenal
Napoli
Barcelona
Atletico Madrid
Monaco
Borussia Dortmund
Leicester
Juventus
Ga jerin wadanda suka yi na biyu a rukuni-rukuni
Paris St-Germain
Benfica
Manchester City
Bayern Munich
Bayer Leverkusen
Real Madrid
Porto
Sevilla



























