Kamaru ta yi watsi da gwanayen 'yan wasanta

Kocin Kamaru Hugo Broos
Bayanan hoto, Hugo Broos ya ki daukar fitattun 'yan wasan Kamaru da yawa zuwa gasar ta kofin Afirka a Gabon
An wallafa

Kocin Kamaru Hugo Broos ya ki sanya sunayen fitattun 'yan wasa da dama a tawagar kasar mai 'yan wasa 23 da za ta je gasar cin kofin Afirka a Gabon a wannan watan.

Daman tuni 'yan wasa bakwai da suka hada da dan bayan Liverpool Jokl Matip da dan wasan gaba na Schalke 04 Eric Choupo-Moting suka ce ba za su je gasar ba.

Dan wasan baya Aurilien Chedjou, na Galatasaray ta Turkiyya na daga fitattun da kocin ya ki sanya wa a tawagar da ta kunshi 'yan wasan gida biyu kawai.

Tun a ranar Talata tawagar ta kamaru, The Indomitable Lions, ta fara atisaye a Yaounde.

Kuma a ranar Alhamis din nan ta yi wasan sada zumunta da gwaji da tawagar Jamhuriyar Dumokuradiyarr Congo, inda ta doke bakin nata 2-0.

Oyongo ne ya ci mata kwallon farko a minti na 53, yayin da Bassogog ya ci ta biyu a minti na 64, a wasan da aka yi a Yaounde.