An tuhumi Man City da kasa bayar da bayanai

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi Manchester City da kasa tabbatar wa wakilan da ke gwada 'yan kwallo kan shan abubuwa masu kara kuzari inda 'yan wasanta suke zuwa.
A dokance an umarci kungiyoyi su bayar da bayanan yadda take yin atisaye da kuma wuraren da 'yan kwallo ke zuwa, domin a gwada su idan an bukaci hakan.
Manchester City ta kasa bayar da cikakkun bayanai kan yadda 'yan kwallonta ke yawace-yawacensu.
An bai wa kungiyar zuwa 19 ga watan Janairu domin ta kare kanta.
Amma ana tsammanin cewar kungiyar ba ta bayar da bayanai ba ne, saboda sauya lokutan atisaye da ta yi.























