Syria na daf da zuwa World Cup

Syria players
Bayanan hoto, Kwallon da Mohamad ya zura wa Iran ta faranta wa 'yan wasan Syria matuka
An wallafa

Syria ta sami damar da zata kai gaci a gasar World Cup na 2018 bayan da tayi kunnen doki 2-2 da Iran a birnin Tehran.

Syria ta bada mamaki bayan da ta shiga gaban Iran, inda dan wasanta Tamer Haj Mohamad ya zura kwallo ta farko da kansa - wanda shi ne karo na farko da aka ci Iran da kwallo, a karkashin kocinta Carlos Queiroz , bayan wasanni 10.

Amma ana daf da tafiya hutun rabin lokaci sai dan wasan Iran, Sardar Azmoun ya rama wa Iran kuma bayan da aka dawo hutun rabin lokaci sai ya kara jefa kwallo ta biyu a ragar Syria.

Amma Syria bata karaya ba, domin Omar Al Somah ya jefa kwallo ta biyu a ragar Iran ana daf da tashi daga wasan.

Su ma Koriya ta Kudu sun yi kunnen doki ne da Uzbekistan, bayan da suka tashi babu ci a wasan rukuni na A wanda ya basu mataki na biyu kuma ya tabbatar musu da nasarar zuwa gasar World Cup ta 2018 a Rasha.

A yanzu Syria zata buga wasanta na gaba da Australiya ko Saudiyya a watan Oktoba, kafin ta kara da wata kungiya daga yankin Concacaf idan tana son ta sami cancantar zuwa wannan gasar ta World Cup a Rasha.

Asia qualifying - Group A

Sharhi

Syriya na da damar zuwa gasar World Cup a Rasha a badi.

A farkon wannan shekarar, BBC ta ziyarci Syria domin hada wani shirin rediyo na kwallon kafa, inda muka kwana shida a birnin Damaskus, kuma mun ga abin mamaki.

Kasar Syria na tsakiyar yakin da aka shafe shekara 6 ana tafkawa, kuma kungiyar kwallon kafa ta kasar bata da kudi saboda takunkumin da aka kakaba wa kasar.

Abin al'ajabin shi ne yadda har suka kai ga wannan gagarumar nasarar duk da irin matsalolin da suke gabansu. Lallai skungiyar ta nuna bajinta da jurewa.

Kasar Malysia suke tafiya idan zasu buga wasansu na gida. wanda kilomita 14,000 kenan zuwa da dawowa daga Syria. A can zasu buga sauran wasannin neman cancanta zuwa gasar ta World Cup.

Syria fans
Bayanan hoto, Dubban 'yan kasar Syria sun kalli wasan a wani babban allo dake filin wasa na Al-Jalaa a birnin Damaskus