Liverpool ta yi rashin nasara kan daukaka karar Mane

Asalin hoton, Rex Features
An wallafa
Liverpool ta yi rashin nasara kan daukaka karar rage wa'adin haramcin da aka yi wa Sadio Mane a wasan da Manchester City ta doke su da ci 5-0.
An kori Mane, mai shekarar 25, daga fili minti 37 da soma wasa bayan ya shuri mai tsaron ragar City Ederson a fuska da kafa.
Dan wasan dan kasar Senegal ba zai buga wasan Premier League da za su yi da Burnley da Leicester ba, da kuma wasan da za su yi a gidan Leicester na cin kofin EFL.
Liverpool za ta buga wasan cin kofin zakarun Turai da Sevilla a ranar Laraba a Anfield.

























