Fifa ta fitar da 'yan wasan da za a zabi 11

Fifa
Bayanan hoto, A ranar 23 za a sanar da 'yan wasan Fifa 11 da babu kamarsu a fagen tamaula
An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta fitar da sunayen 'yan wasa 55, wadanda a cikinsu za a zabi 'yan wasa 11 da babu kamarsu a fagen tamaula a duniya.

Real Madrid ce ke da 'yan wasa mafi yawa - guda 12 - kuma masu buga gasar La Liga 23 ne ke cikin 'yan takara.

'Yan wasan da suke buga gasar Premier 13 ne ke cikin sunayen da Fifa ta fitar da dan kwallon Wales mai taka-leda a Real Madrid Gareth Bale.

Za a bayyana 'yan wasan Fifa 11 a wani bikin karrama wadan da suka bayar da gudunmawa a fagen kwallon kafa da za a yi a Landan a ranar 23 ga watan Oktoba.

Kimanin kwararrun 'yan wasa 25,000 daga kasashe 75 ne suka fitar da 'yan wasan da za a zabi fitattu 11 da babu kamarsu a fagen tamaula a duniya.