Everton ta ci tarar Rooney albashin mako biyu

An wallafa
Kungiyar Everton ta ci tarar Wayne Rooney kudin albashin mako biyu, za kuma ta bai wa mabukata, bayan da aka samu dan kwallon da laifin tuki a cikin maye.
Everton ta ce za ta bayar da kudin da zai kai fam 300,000 domin a yi wasu ayyukan jin kai a birnin na Everton domin kyautata rayuwar al'umma.
Rooney ya nemi afuwa ga magoya baya da iyalai bayan da aka hukunta shi.
An haramta wa dan kwallon mai shekara 31 yin tukin mota na tsawon shekara biyu, an kuma umarce shi da yin aikin baban-giwa na sa'a 100 ba tare da an biya shi ba, a matsayin cikon umarnin da kotun ta ba shi na yi wa al'ummarsa hidima.
Haka kuma an umarce shi da biyan fam 170 a lokacin da ya gurfana a kotun majistare a Stockport.























